Sanatoci sun sallama albashinsu na Disamba ga nutanen Tudun Biri

0
279

Sanatocin Najeriya gaba ɗayansu sun sadaukar da albashinsu na watan Disamba ga mutanen da harin bom da jirgin soji ya samu a wurin taron Mauludi a Jihar Kaduna.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya sanar cewa sanatocin su 109 sun amince a ba da albashin nasu a matsayin gudunmuwar ga mutanen Tudun Biri.

Sanata Barau wanda ya yi bayani a yayin ziyararsu fadar gwamnatin Kaduna domin jajanta wa Gwamna Uba Sani  kan tsautsayi, ya bayyana cewa albasjin ya kama naira miliyan 109.

Ya ce hakika sun yi baƙin ciki bisa tsautsayin da ya auka wa al’ummar garin na Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi, kuma majalisar ta sha alwashin yin bincike domin gano musabbabin abin da ya faru.

KU KUMA KARANTA: Za mu jajirce har sai an yi wa mutanen Tudun-Biri adalci – Sarkin Musulmi

Gwamna Uba Sani a jawabinsa ya miƙa godiyarsa ga dukkan ’yan majalisar da suka jajanta masa, inda ya buƙaci su tabbatar da Hakimin Yan Tudun Biri ya fito kunya ta hanyar yi musu adalci.

Ya kuma nuna rashin jin daɗinsa bisa yadda wasu ke neman sanya rigar addini ko ƙabilanci a kan abin da ya faru, inda ya ce abin ba haka yake ba.

Leave a Reply