Sanatoci Sun Amince Da Kara Sabbin Makaratun Koyon Aikin Lauya 7 A Najeriya

0
306

Daga; Rabo Haladu.

MAJALISAR Dattawa ta amince da kudurin dokar kafa karin makarantun koyon aikin lauya a yankuna shidana kasar nan.

Majalisar ta amince da kudurin a zaman da ta yi yau Talata, 8 Fabrairu na 2022, bayan nazarin rahoton kwamitinta a kan harkokin shari’a da hakkin dan-Adam.

Makarantun da ake da su a yanzu su ne wadda take a Abuja; yankin arewa ta tsakiya, sai ta Kano, wadda ke Bagauda; yankin arewa maso yamma, sai ta Yola; yankin arewa maso gabas, sai ta Lagos; yankin kudu maso yamma da ta Enugu; yankin kudu maso gabas, da kuma ta Yenegoa a yankin kudu maso kudu.

Wadanda aka amince a kara sun hada da wadda za a yi a Kabba, Jihar Kogi a arewa ta tsakiya, da wata a Jos a yankin arewa maso tsakiyar ita ma, da ta Maiduguri a Jihar Borno domin arewa maso gabas, sai ta Argungu a Jihar Kebbi yankin arewa maso yamma.

Sauran su ne ta Okija a Jihar Anambra a yankin kudu maso gabas sai ta Orogun a Jihar Delta yankin kudu maso kudu, sai kuma ta Ilawe da ke Jihar Ekiti a kudu maso yamma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here