Sanata Yari ya raba raguna 500 ga maƙwabta

0
280

Sanata Abdul’aziz Yari (APC-Zamfara) ya raba raguna 500 ga maƙwabtansa da iyalai marasa galihu a garin Talata-Mafara da ke ƙaramar hukumar Talata-Mafara a jihar domin gudanar da bukukuwan Sallah Eid-el-Kabir.

Shugaban kwamitin rabon kayayyakin, Sha’aya Sarkin-Fawa ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da ragon ga waɗanda suka amfana a ranar Alhamis a Talata-Mafara.

“Kun sani, wannan shiri ne na shekara-shekara daga shugabanmu, Sanata Yari da nufin taimaka wa gidaje marasa galihu don gudanar da bukukuwan Sallah cikin sauƙi.

“Wannan na maƙwabtansa ne, gidaje marasa galihu, ‘yan gudun hijira (IDP) da marayu a cikin garin Talata-Mafara kawai.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin jihar Kano za ta biya wa ɗalibai 55,000 kuɗin rubuta jarabawar NECO

“Wannan baya ga raguna 1,000 da shanu 400 da ya bayar a baya ga shugabannin jam’iyyar APC a matakin Jiha, ƙananan hukumomi, da unguwsnni a faɗin jihar ta hanyar ƙungiyarsa ta siyasa.” Inji shi.

Sarkin-Fawa, jigo a jam’iyyar APC a jihar, ya yaba wa tsohon gwamnan bisa shirye-shiryensa na shiga tsakani da tattalin arziƙi daban-daban da yake tallafa wa jama’a a matakin ƙasa.

Ya kuma yi ƙira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da lokacin Eid-El-Kabir wajen yin addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da ma Najeriya baki ɗaya.

Leave a Reply