No menu items!

Sample Page Title

Date:

Sanata Ndume ya gana da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa

Daga Ali Sanni

Sanata Mohammed Ali Ndume, wanda ke wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya gana da Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Ganawar ta gudana ne a babban ofishin APC na ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.

Idan ba a manta ba an tsige Ndume daga muƙamin mai tsawatarwa na Majalisar Dattawa, bayan ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu game da halin yunwa da yan ƙasar ke fama dashi.

Matakin ya biyo bayan wasiƙar da Ganduje ya aike wa majalisar, sannan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya karanta a zauren majalisar.

An maye gurbin Ndume da Sanata Tahir Monguno, wanda ke wakilar Borno ta Arewa a matsayin sabon mai tsawatarwar majalisar.

KU KUMA KARANTA: Ni ba ɗan yawan buɗe ido ba ne – Sanata Ndume

Monguno, ya kuma zama Mataimakin Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Dattawa, muƙamin da Ndume ya riƙe kafin a tsige shi.

Magoya bayan Ndume sun gudanar da zanga-zanga kan buƙatar Majalisar Dattawa da APC su dawo da shi kan muƙamin nasa.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...