Sanata Bomoi ya ba da gudumawar naira miliyan ɗaya ga asibitin ƙwararru na Potiskum don daƙile cutar mashaƙo

1
415

Daga Ibraheem El-Tafseer

Sanata Ibrahim Mohammed Bomoi, Sanata mai wakiltar Yobe ta Kudu, ya ba da gudumawar naira miliyan ɗaya don a ci gaba da daƙile yaɗuwar cutar mashaƙo (diphtheria) wadda take kashe ƙananan yara a garin na Potiskum da maƙwabtanta. Hukumar Kula da Asibitin Ƙwararru na Potiskum ya yaba wa Sanatan bisa ga irin wannan nuna da damuwa da halin da al’ummar ke ciki.

Daraktan kula da lafiya na Asibitin, Dakta Ayuba Zakar, wanda ya bayyana jin daɗin da Hukumar Asibitin ta ji ga Neptune Hausa, ya bayyana irin tasirin tausayi da goyon bayan Bomai a lokacin da suke cikin mawuyacin hali.

Ya ce, “Kuɗaɗen sun taimaka wajen samun magungunan da ake buƙata sosai, tare da sanya fata da ƙwarin gwiwa a zukatan ƙwararrun masana kiwon lafiya da ma marasa lafiya baki ɗaya.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Yobe tana cigaba da daƙile cutar mashaƙo a jihar

Muna da cikakkiyar masaniya kan jajircewar Sanata Bomai wajen yi wa jama’ar mazaɓarsa hidima da kare muradunsa. Gudumawar da ya bayar a baya-bayan nan ga waɗanda suka kamu da cutar amai da gudawa ta misalta yadda yake sadaukar da kai ga lafiya da jin daɗin jama’a.

Ina tabbatar wa jama’a cewa muna bakin ƙoƙarinmu don ganin an daƙile ɓarkewar cutar mashaƙo a Potiskum. An yi amfani da gudummawar nan take don sayan magunguna da sauran abubuwan da suka dace don taimaka wa marasa lafiya su samu murmurewa,” inji Ayuba.

Babban jami’in kula da ma’aikatan jinya (Chief Nursing Officer) na Asibitin Bukar Anguwa ya jaddada ci gaban da aka samu tun lokacin da aka samu kuɗaɗen, inda ya ƙara da cewa hakan zai ƙara ƙarfafa ƙoƙarin da asibitin ke yi na daƙile ɓarkewar cutar.

Har ila yau, Abubakar Adamu Baba, wanda shi ne ya karɓi tallafin, ya tabbatar da cewa Sanata Ibrahim ya kasance mai goyon bayan asibitin, wanda ya saba bayar da irin wannan gudumawa tun kafin ya shiga siyasa.

A nasa ɓangaren, babban jami’in kula da ma’aikatan jinya Bukar Anguwa, ya jaddada ci gaban da aka samu tun bayan samun tallafin da Sanata Bomai ya yi masa, ya ƙara da cewa hakan zai taimaka matuƙa wajen daƙile annobar.

Wanda ya wakilci Sanata Bomai a wajen, Ibrahim Mohammed (Ibbiyo) ya tabbatar da cewa ƙoƙarin da Sanatan ke yi na bayar da gudunmawa ga ci gaban al’umma ya kasance a kodayaushe.

Hakazalika, Asibitin ya yaba wa Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, bisa namijin ƙoƙarinsa na bayar da tallafi a wannan lokaci mai cike da ƙalubale.

Baya ga gudunmawar da Sanata Bomai ya bayar, asibitin ya kuma nuna jin daɗinsa ga Hukumar Lafiya ta Duniya, Ayyukan Yaƙi da Yunwa, da UNICEF bisa gagarumin gudunmawar da suke bayarwa wajen magance matsalar cutar mashaƙo a jihar Yobe da kewaye.

Har ila yau, ta amince da tallafin da aka samu daga Dakta Lawan Gana, babban mataimaki na musamman ga gwamna Buni kan harkokin kiwon lafiya, da kuma Dakta Musa Baba, babban sakataren hukumar kula da asibitoci, Dakta Umar Chiroma, daraktan kula da lafiya a matakin farko, da kuma masanin cutar a jihar Yobe.

Idan za a iya tunawa a baya Neptune Hausa ta bayar da rahoton cewa cutar mashaƙo da ake kyautata zaton ta ɓulla a jihar Yobe ta yi sanadiyar mutuwar aƙalla yara 30, yayin da wasu ƙarin 42 ke kwance a cibiyar keɓewar asibitin ƙwararru na Potiskum, yayin da cutar ta fi ƙarfi a yankunan Tandari, Misau Road, Sabuwar Sakateriya, Arikime, Ramin Ƙasa, Boriya, Uganda, da unguwar Texaco.

1 COMMENT

Leave a Reply