Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya ɗauki matakai don dakatar da yunkurin Shoprite, ɗaya daga cikin fitattun manyan kantunan Najeriya daga rufe reshensa na jihar Kano.
Alfijir labarai ta rawaito Shahararren kantin sayar da kayayyaki na Shoprite dake Ado Bayero Mall ya sanar da matakin rufewa daga jihar Kano a watan Janairu, inda ya ɗora laifin ga yanayi na ƙalubalen tattalin arziki.
Jama’a da dama suna ta bayyana ra’ayoyinsu dangane da hukuncin da kantin ya ɗauka, wanda kuma ya fara gudanar da harkokin kasuwancin sa a Kano a watan Maris na 2014.
Wata sanarwa da mai baiwa Sanata Barau shawara kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kan jama’a Ismail Mudashir ya fitar, ta ce mataimakin shugaban majalisar dattawan zai gana da mahukuntan kamfanin a cikin makon nan a Abuja don shawo kan lamarin.
KU KUMA KARANTA: Dalilin da ShopRite zai bar Kano
‘’Eh, batun kasuwanci ne tsantsa, amma za mu ga abin da za mu iya yi don ƙarfafa musu gwiwa su janye shawarar da suka yanke ta barin Kano, don su ci gaba da zama a birnin na dabo.
Tabbas kamar yadda kowa ya sani, akwai tarin damammakin kasuwanci a cibiyar kasuwanci ta Arewacin Najeriya. In Ji sanatan, don haka zamu yi mai yiwuwa wajen daidaita lamarin.