Sama da yara 13,000 Isra’ila ta kashe a Gaza – UNICEF

0
119

Hukumar kula da ƙananan yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sama da yara 13,000 aka kashe a Gaza a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa, inda ta ƙara da cewa yara da dama na fama da rashin abinci mai gina jiki kuma ba su da kuzarin yin kuka.

Dubban mutane sun jikkata ko kuma ba za mu iya tantance inda suke ba. Wataƙila sun maƙale a karkashin ɓaraguzan gine-gine … Ba a taɓa samun yanayin da aka kashe yara da yawa haka ba a duk wani rikici a duniya,” in ji Babbar Daraktar UNICEF. Catherine Russell ta shaida wa shirin “Face the Nation” na CBS News.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe tare da jikkata mutane da ‘dama’ da ke jiran agajin abinci a Gaza

“Na kasance a cikin dakunan yara masu fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki, duk dakin ya yi shiru. Saboda yara da jarirai … ba su da kuzarin yin kuka.”

Russell ya ce akwai “gaggarumin ƙalubale na tsarin mulki” ga manyan motoci masu jigilar kayan abinci zuwa Gaza don ba da agaji.

Leave a Reply