Sama da mutane miliyan 73 ne ke fama cutar ruɓewar haƙora a Filipin

0
317

Aƙalla ’yan ƙasar Filifin (Philippines) miliyan 73 ne ke fama da ciwon haƙori, abin da ya sa cutar ta zama “mummunan damuwar kiwon lafiya” a ƙasar kudu maso gabashin Asiya, in ji Ma’aikatar Lafiya ta Philippines, DOH, a ranar Laraba.

“Cutar hakori annoba ce ta shiru,” in ji Manuel Vallesteros, babban jami’in sashen kula da rigakafin cututtuka na DOH, ya bayyana hakan bayan wani taron kwamitin a majalisar wakilai.

KU KUMA KARANTA: Sama da mutane miliyan ɗaya sun rasa muhallansu a Somaliya – Hukumomin agaji

Vallesteros ya ce bayanan DOH sun dogara ne akan binciken lafiya na ƙasa na 2018, tare da lura cewa adadin yanzu ya fi girma idan aka kwatanta da lokacin da cutar ta COVID-19 ta hana samun sabis na haƙori sama da shekaru biyu.

Ya lura cewa takwas daga cikin 10 na Filipinas suna fama da “caries na yara” ko “ruɓewar haƙoran jarirai” saboda ana ciyar da su da kayan abinci mai zaƙi.

“Halin lafiyar baki na yaran Filipin yana da ban tsoro,” in ji DOH, ta ƙara da cewa cutar baki “ya ci gaba da zama babbar matsalar lafiyar jama’a” a Philippines.

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, (WHO), ciwon haƙori babbar matsala ce ta lafiyar jama’a a duniya kuma cuta ce da ta fi yaɗuwa.

Leave a Reply