Yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza yana barin dubban mata masu juna biyu na kokawa da mummunan yanayin tsafta da kuma hadarin lafiya, in ji hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNRWA.
“Fiye da mata masu juna biyu 150,000 na fuskantar mummunan yanayi na tsafta da kuma hadurran lafiya a cikin yanayin ƙaura da kuma yaƙi,” in ji UNRWA a cikin wata sanarwa.
KU KUMA KARANTA: Sojojin Isra’ila sun kama Falasɗinawa 28 a Gabar Yamma da Kogin Jordan
Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya ta wallafa hoton wata yarinya sabuwar haihuwa a yankin da yaki ya daidaita.
“An haifi Habiba a cikin wani karamin tanti. Tana da sati biyu, kuma nauyinta bai wuce kilogiram biyu ba,” in ji shi. “Babu wani yaro a duniya da ya isa ya sha wahala haka.”