Sakatare Janar na MƊD ya koka kan rashin zaman Afirka mamba ta dindindin a Kwamitin Tsaro

0
117

Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya caccaki Kwamitin Tsaro na Majalisar bisa rashin bai wa Afirka kujerar mamba ta dindindin a cikinsa.

‘Ta yaya za a amince da matakin hana bai wa Afirka mamba ta dindindin a Kwamitin Tsaro?’ in ji Antonio Guterres a saƙon da ya wallafa a shafin X.

“Dole ne ƙungiyoyi su yi nazari kan halin da duniya take ciki a yau, ba abin da ya faru ba shekaru 80 da suka wuce. Taron da za a yi a watan Satumba zai bayar da wata dama ta duba batun sauye-sauyen shugabancin duniya da sake ƙulla alaƙa bisa gaskiya,” a cewarsa.

Guterres ya jaddada ƙiran da ya yi na kai kayan agaji da kuma tsagaita wuta a Gaza tare da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

KU KUMA KARANTA: Australia ta goyi bayan ƙudurin MƊD na tsagaita wuta a Gaza

“Ba zan yi ƙasa a gwiwa ba wurin yin ƙira a tsagaita wuta nan-take da kai kayan agaji da kuma sakin dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su ba tare da wasu sharuɗɗa ba,” in ji shi.

Da yake tsokaci kan halin da ake ciki a Gaza wadda ke ci gaba da fuskantar hare-haren Isra’ila, ya ce: “Al’ummar Gaza suna mutuwa sakamakon harin bama-baia da rashin abinci da wuta da kuma rashin hasken lantarki a asibitoci da rashin magunguna.”

Leave a Reply