Connect with us

Ƙasashen Waje

Sakamakon zaɓe ya nuna cewa ƴan Rasha sun amince da jagorancina – Putin

Published

on

Vladimir Putin ya sanar da cewa nasarar da ya samu a zaɓen shugaban ƙasar Rasha – bayan zaɓen da bai fuskanci wata adawa mai ƙarfi ba – ta nuna cewa ƴan ƙasar sun aminta da jagorancinsa.

“Ina so na yi godiya a gare ku baki ɗaya kan goyon baya da amincin da kuka nuna mani,” kamar yadda Putin ya bayyana a ranar Litinin da safe a wani taron manema labarai a hedikwatar yaƙin neman zaɓensa da ke Moscow.

“Ina so na yi godiya ga ƴan ƙasar Rasha… waɗanda suka zo rumfunan zaɓe inda suka kaɗa ƙuri’a,” kamar yadda Putin ya bayyana bayan sakamakon farko ya nuna cewa shi ne ke kan gaba bayan ya samu kashi 87 cikin 100.

KU KUMA KARANTA: Amurka da Rasha za su yi magana kan mamayar Isra’ila a babbar kotun MƊD

A daidai lokacin da yaƙi da Ukraine ya shiga shekara ta uku, ya yi godiya ta musamman “ga sojojinmu.. waɗanda suka cika alƙawari mafi muhimmanci da suka ɗauka wanda shi ne kare jama’ar ƙasa”.

“Ko wane ne ko kuma duk yadda suke so su tsoratar da mu, kuma duk wanda yake so ya daƙile mu ko niyyar mu – babu wanda ya taɓa yin haka a tarihi. Hakan bai yi aiki a yanzu ba kuma ba zai yi a nan gaba ba.” kamar yadda Putin ya bayyana a wani jawabi ta talabijin.

Putin ya kuma bayyana cewa mutuwar tsohon jagoran yan adawa na ƙasar “lamari ne maras daɗi” inda ya ce har an shirya sakinsa ta hanyar musayar fursunoni.

Ya ce, “dangane da Mr. Navalny. Eh, ya rasu. Wannan lamari ne maras daɗi.” Ya ƙara da cewa “kwanaki kaɗan kafin Mr. Navalny ya rasu, wasu daga cikin abokan aiki sun shaida mani cewa… akwai batun musayar fursuna da Navalny inda za a musaya shi da wasu fursunoni da ke ƙasashen Yamma… sai na ce na amince.”

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ƙasashen Waje

Mutumin da ya fi kowa tsallake haɗari a duniya ya mutu

Published

on

Mutumin da ya fi kowa tsallake haɗari a duniya ya mutu

Mutumin da ya fi kowa tsallake haɗari a duniya ya mutu

Daga Ibraheem El-Tafseer

Frane Selak ya kasance wanda ya fi kowa tsallake rijiya da baya a duniya.

A shekarar 1962 ya tsallake haɗarin jirgin ƙasa wanda mutane 17 suka mutu, a 1963 jirgi ya faɗi da shi kowa ya mutu sai shi kaɗai ko ƙwarzane bai yi ba.

A shekarar 1966 motar safa ta lume da su a rafi mutum huɗu sun mutu amma Frane bai samu ko ƙwarzane ba a yayin da a shekarar 1973 motarsa ta kama da wuta ya tsallake rijiya da baya, ya kuma tsallake haɗarin taho mu gama da mota ta yi da shi ya tsira ya kuma lashe yuro dubu ɗari takwas a Caca a shekarar 2003.

KU KUMA KARANTA: Labarin zuwa Hajji mai ban mamaki

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza

Published

on

Isra'ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza

Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza

Isra’ila ta ƙaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Gaza, inda ta tilasta wa ɗaruruwan Falasɗinawa tserewa bayan da soji suka kuma ba da umarnin ƙaurace wasu yankuna masu yawan jama’a.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Isra’ila sun ce an yi musayar wuta da dakarun Masar

Waɗanda suka shaida lamarin sun ce an kai hari da dama a ciki da wajen birnin Khan Younis, inda aka hallaka mutane takwas kuma mutane sama da 30 suka samu raunuka, cewar wata majiyar lafiya da kuma ƙungiyar Red Crescent ta Falasɗinawa.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Farashin man fetur zai ƙaru a watan Yuli a Ghana – COPEC

Published

on

Farashin man fetur zai ƙaru a watan Yuli a Ghana - COPEC

Farashin man fetur zai ƙaru a watan Yuli a Ghana – COPEC

Ƙungiyar Kare Haƙƙin Masu Amfani da Man Fetur a Ghana ta yi hasashen cewa akwai yiwuwar a samun ƙarin farashin man fetur a ƙasar a farkon watan Yulin 2024.

Ƙungiyar ta Chamber for Petroleum Consumers (COPEC) ta ce akwai alamu masu ƙarfi da ke nuna cewa farashin fetur da man dizel da gas zai ƙaru baki ɗaya a gidajen man da ke faɗin ƙasar, kamar yadda kamfanin watsa labarai na ƙasar Ghana ya ruwaito.

COPEC ɗin ta ce za a samu ƙarin farashin ne sakamakon yadda farashin Cedi ɗin a ƙasar ke ƙara karewa idan aka kwatanta da dalar Amurka.

COPEC ɗin ta yi hasashen cewa farashin man fetur ɗin wanda za a rinƙa sayarwa a gidan mai zai ƙaru da kashi 2.17 cikin 100, wanda hakan ke nufin zai ƙaru daga Cedi 14.17 zuwa Cedi 15.20 a duk lita.

Sai kuma farashin dizel ana sa ran ya ƙaru zuwa 15.21 a kowace lita ɗaya, sai kuma na gas ya koma tsakanin Cedi 13.24 zuwa Cedi 14.64 a duk kilo ɗaya.

KU KUMA KARANTA: Ɗan Ghana ya kafa tarihi na rungumar bishiyoyi a duniya

Ƙungiyar ta COPEC ta bayar da shawara ga gwamnatin Ghana da ta yi duk mai yiwuwa domin rage harajin da yake a kan gas ko kuma yin tallafi a farashinsa domin bayar da dama ga ‘yan ƙasar su same shi a farashi mai rahusa.

Ta kuma yi ƙira ga gwamnati da kada ta yi ƙasa a gwiwa wajen dawo da matatar mai ta Tema a kan aiki (TOR) don kaucewa ko kuma rage shigo tattacen man fetur wanda a wani lokacin ake samun gurɓatacce.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like