Sakacin gwamnati ne da jami’an tsaro kan kisan Sarkin Gobir – Atiku

0
78
Sakacin gwamnati ne da jami'an tsaro kan kisan Sarkin Gobir - Atiku

Sakacin gwamnati ne da jami’an tsaro kan kisan Sarkin Gobir – Atiku

Daga Ali Sanni Larabawa

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin ƙasar da sakaci kan kisan da aka yiwa Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa.

A ranar Laraba ne jaridar Neptune Prime Hausa ta kawo muku rahoto akan ’yan bindigar da sukayi garkuwa dashi suka kuma kashe shi, bayan kasa kai musu kuɗin fansar da suka buƙata domin sakin sarkin tare da ɗansa.

Shuaibu Gwanda Gobir, wanda shi ne Magaji Garin Gobir kuma ɗaya daga cikin masu naɗin sarki, yace labarin ya isso su cewa masu garkuwar sun kashe sarkin ne a ranar Talata.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe Sarkin Gobir, Isa Bawa 

Sai dai cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon shugaban ƙasar, yace sakacin gwamnati da na jami’an tsaro ne suka janyo mutuwar sarkin.

“Nuna halin ko’in kula da gwamnati ta yi, da rashin ingantaccen tsari daga jami’an tsaro sun taimaka wajen yaɗuwar irin waɗannan abubuwan masu sanya raɗaɗi a zuciya a lokutan baya-bayan nan,”

“Yana da muhimmanci mu ƙara jaddada wa gwamnati cewa dole ne ta samar da tsaron rayukan jama’a ta yadda mutane ba za su rayu cikin fargabar fuskantar irin haka ba.”

Atiku Abubakar ya nuna alhininsa kan rasuwar sarkin tare da miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalai da ɗaukacin al’ummar masarautar Gobir, da Gwamnatin Sakkwato kan mutuwar sarkin da ya bayyana a matsayin mai “cike da tashin hankali.”

A cikin wannan makon ne dai aka ga sarkin a wani bidiyo yana neman Gwamnatin Sakkwato ta biya ’yan bindigar kuɗin fansar da suka buƙata, inda ya ce idan wa’adi ya cika ba’a biya ba zasu halaka shi.

Makonni uku da suka gabata ne ’yan bindigar suka yi garkuwa da sarki a yankin Kwanar Maharba, lokacin da yake kan hanyar komawa gida bayan  halartar wani taro a cikin garin Sakkwato.

Leave a Reply