Sai na jawo Tinubu ya yi asarar ƙuri’u sama da miliyan 1 a zaɓen 2027 – Sanata Kabiru Marafa
Tsohon Ɗan Majalisar Dattawan Najeriya mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya, Sanata Kabiru Marafa ya sha alwashin rage wa Tinubu ƙuri’u masu yawa a zaɓen 2027.
Marafa, wanda a baya-bayan nan ya sanar wa BBC ficewarsa daga jam’iyyar APC, bayan ya zargi Tinubu da ”watsar da shi bayan cin zaɓe” ya ce sai ya kawo wa shugaban ƙasar cikas a zɓen 2027 da ke tafe.
KU KUMA KARANTA: A lissafin da na yi, Tinubu na uku zai zo a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 – El-Rufai
Yayin wata hira da hgidan talbijin na Channels, Sanata Marafa ya ce sai ya janyo wa Tinubu asarar kimamin ƙuria’ miliyan guda.
Tsohon ɗan majalisar – wanda ya kasance babban daraktan yaƙin neman zaɓen Tinubu a Zamfara a 2027 – ya ce zai nuna wa shugaban ƙasar matsayinsa a siyasar jihar Zamfara.









