Sabon Gwamnan Kano Abba Gida-Gida, ya naɗa shugaban ma’aikata da sakataren gwamnati

3
980

Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya naɗa Sagagi a matsayin shugaban ma’aikata, Baffa Bichi a matsayin Sakataren Gwamnatin jihar, Laminu Rabiu a matsayin babban sakatare na hukumar Alhazai (ES).

Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, ya nada tsohon shugaban jam’iyyar PDP reshen Kano, Shehu Sagagi da kuma tsohon babban sakataren asusun kula da manyan makarantu, TETFUnd, Baffa Bichi a matsayin shugaban ma’aikata kuma sakataren gwamnatin jihar.

Gwamnan ya kuma naɗa Farouq Kurawa da Abdullahi Rogo a matsayin babban sakatare mai zaman kansa da kuma babban jami’in hulɗa da jama’a.

KU KUMA KARANTA: Lawal-Falala ya zama Kwamandan NSCDC na Kano

Sanusi Dawakintofa, wanda ya kasance mai magana da yawun gwamnan a duk lokacin yaƙin neman zaɓe da lokacin miƙa mulki, an naɗa shi a matsayin babban sakataren yaɗa labarai na sabon gwamnan.

Wata sanarwa da Dawakintofa ya fitar ta ce naɗin ya fara aiki ne daga ranar Litinin 29 ga Mayu, 2023.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an zaɓo waɗanda aka naɗa ne bisa la’akari da yadda suka jajirce da kuma biyayyarsu.

A wata sanarwa da ya fitar a safiyar ranar Talata, gwamnan ya naɗa Yusuf Lawan da Laminu Rabiu a matsayin shugaban hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kano.

Membobin kwamitin da gwamnan ya naɗa sun haɗa da Abbas Abubakar Daneji, Shehi Shehi-Maihula, Munir Lawan, Isma’il Mangu, Aishatu Munir Matawalle da Sani Ashir.

A cewar sanarwar, waɗanda aka naɗa za su ɗauki nauyin gudanar da harkokin hukumar cikin gaggawa domin ganin an samu nasarar gudanar da aikin Hajjin 2023.

3 COMMENTS

Leave a Reply