Sabbin sarakunan Rano da Ƙaraye masu daraja ta biyu sun yi mubaya’a ga Sarki Sanusi

0
55
Sabbin sarakunan Rano da Ƙaraye masu daraja ta biyu sun yi mubaya’a ga Sarki Sanusi

Sabbin sarakunan Rano da Ƙaraye masu daraja ta biyu sun yi mubaya’a ga Sarki Sanusi

Daga Idris Umar, Zariya

Sabbin sarakunan Rano da Ƙaraye masu daraja ta biyu da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa a matsayin masu daraja ta biyu, sun yi mubaya’a ga Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II a ranar Laraba.

Sun kai wa sarki Sanusi II ziyarar ne sa’o’i kaɗan bayan Gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana naɗin nasu.

Sabbin sarakunan sun haɗa da, Alhaji Muhammad Maharaz na Ƙaraye, Muhammad Isah Umar na Rano, da Alhaji Aliyu Abdulkadir na Gaya.

Sun yi mubaya’a ga Sarki Sanusi a zaman fadar da aka gudanar ranar Laraba.

Duk sarakunan biyu sun yi alƙawarin yin aiki a ƙarƙashin masarautar Kano mai daraja ta ɗaya tare da gode wa Gwamna Abba Yusuf bisa ganin sun cancanta har ya naɗa su .

KU KUMA KARANTA: Shekara ɗaya tayi wa Tinubu kaɗan ya warware matsalolin da ya gada – Sarki Sanusi

Idan za a iya tunawa, a ranar jiya talata 16 ga Yuli, 2024, Gwamnan ya rattaɓa hannu a kan dokar kafa masarautu masu daraja ta biyu a jihar.

Masarautar Rano da ta ƙunshi ƙananan hukumomin Rano, Kibiya, da Bunkure; sai masarautar Gaya da ta ƙunshi ƙananan hukumomin Gaya, Ajingi, da Albasu; ita kuma Ƙaraye ta ƙunshi ƙananan hukumomin Ƙaraye da Rogo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here