Sabbin Hafsoshin tsaro sun gana da Ministan tsaro, Badaru
Ministan Tsaro na ƙasa, Mohammed Badaru Abubakar ya karɓi sabbin shugabannin rundunonin tsaro na ƙasa a ofishin sa a yau Talata a Abuja.
Cikin waɗanda suka halarta akwai Babban Hafsan Tsaro, Laftanar Janar OO Oluyede; Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Mejar Janar W. Shaibu; Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Rear Admiral I. Abbas; da Babban Hafsan Sojojin Sama, Air Vice Marshal S. K. Aneke.
KU KUMA KARANTA: Ministan tsaron Badaru ya halarci babban taron ƙungiyar ‘yan kasuwa ta ƙasa a Kwara
Hadimin Ministan Safwan Sani Imam ya ce Ziyarar ta nuna kudirin Ministan na ƙarfafa haɗin kai da haɗin gwiwa tsakanin rundunonin tsaro domin kare martabar ƙasar da tabbatar da tsaron iyakokinta, bisa jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.









