Saƙon Dr. Nasiru Gawuna ga al’ummar Kano bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara

0
230

Ɗan takarar gwamnan Kano na jamiyyar APC da kotu ta ce shi ne yayi nasara a zaɓen gwamnan Kano na 2023 Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya buƙaci magoya bayansa da su ƙara dagewa da addu’o’i domin samun nasara a kotun ƙolin.

Alfijir Labarai ta rawaito Gawuna ya faɗi haka ne ta cikin wani saƙo da ya sanyawa hannu da kansa.

Yayi godiya ga shugaban jamiyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Kano Dr. Abdulkahi Umar Ganduje bisa yadda ya yita kokarin ganin sun samu nasara a kotu.

Nasiru ya kuma yabawa magoya bayan jamiyyasa APC a kano bisa yadda suka jajirce.

Ya kuma godewa alummar Kano bisa irin kyakykyawan zaton da suke yi masa.

KU KUMA KARANTA: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da Gawuna a matsayin gwamnan Kano

“Ina godewa kotun ɗaukaka ƙara saboda yadda tabbatar da gaskiya ta hanyar jaddada hukuncin da kotun sauraren ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar kano ta yanke tun ranar 20 ga watan Satumbar wannan shekara”. Inji Gawuna

Ya ƙara da cewar, abun da alkalan kotun nan tirabunal da kotun ɗaukaka ƙara sukai na tabbatar da gaskiya cigaba ne ga dimokuraɗiyya, sannan kuma hakan ya nunawa duniya cewa kotu ita ce gatan mara gata.

“Ina godiya tare da yabawa mataimakin Shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata Barau Jibril da Ministocinmu guda biyu da shugaban jam’iyyar APC na jihar kano Abdullahi Abbas , sai Malamai ‘yan kasuwa da duk al’ummar jihar kano bisa goyon bayan da suka bamu har muka sami wannan nasarar “. A cewar Dr. Nasiru Gawuna

Leave a Reply