Ruwan sama ya lalata gidaje da dama a garin Faguji, jihar Bauchi

0
105
Ruwan sama ya lalata gidaje da dama a garin Faguji, jihar Bauchi

Ruwan sama ya lalata gidaje da dama a garin Faguji, jihar Bauchi

Daga Idris Umar, Zariya

Rahotanni sun tabbatar da cewa kwanaki uku akayi ana zabga ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, a garin Faguji dake ƙaramar hukumar Gaiɗe ta jihar Bauchi.

Wannan yanayi ya jefa al’ummar yankin cikin mawuyacin hali na rashin matsuguni ga kuma wahalar rayuwa ta yau da kullum musamman hauhawar farashin kayan abinci da sauran kayan al’amuran yau da kullum.

Mutanen garin sun shiga cikin damuwa bisa yadda gidaje ke faɗuwa babu ƙaukautawa sakamako yadda ruwa ya shafe wasu unguwanni da yawa a yankin.

KU KUMA KARANTA;Ambaliya ta yi ɓarna a jihohi 20, wasu 13 na cikin haɗari

Yanzu haka katangu da ɗakunan mutane sai zubewa sukeyi, Rijiyoyi da shadda duk sun cika da Rauwa.

Amma ya zuwa haɗa wannan rahoton mazauna yankin sunce, sunasa rai tare da tabbacin hukumomi sun sami labarin lamarin da suke ciki kuma suna sa rai da za a kawo masu taimakon gaggawa da ikon Allah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here