Rundunar ‘yansandan Kano ta tura mutane 333 da ake zargi da tayar da rigima a wajen zaɓen cike-gurgi 

0
465
Rundunar 'yansandan Kano ta tura mutane 333 da ake zargi da tayar da rigima a wajen zaɓen cike-gurgi 

Rundunar ‘yansandan Kano ta tura mutane 333 da ake zargi da tayar da rigima a wajen zaɓen cike-gurgi

Daga Jameel Lawan Yakasai

Rundunar ‘yansanda ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta kama mutane 333 da ake zargi da ta da tarzoma a yayin zaɓen da aka cike-gurgi na Ghari/Tsanyawa da kuma zaɓen cike gurbi na Bagwai/Shanono da aka gudanar ranar Asabar, 16 ga Agusta, 2025.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, wanda ya gabatar da jawabi ga manema labarai a Kano yau Litinin, ya ce an kama wadannan mutane ne da makamai da kayan tada rikici da suka hada da:

Bindiga Pump Action guda 1

Bindigogi na gida 5

Wukake 18, Takubba 16, Adduna 18

Barandami 32, Gora 94

Kibiya da baka, gatari da duwatsu 45

Motoci 14

Akwatin kuri’a guda 2, da takardun kuri’a da aka riga aka yi musu alamar zabe 163

Kudi naira miliyan 4 da dubu 48.

KU KUMA KARANTA: Zaɓen cike gurbi a Kano: An kama ‘yan daba sama da 100 da ake zargi da yunƙurin tayar da tarzoma – INEC

CP Bakori ya ce duk wadanda aka kama an gurfanar da su gaban kotunan majistire daban-daban a Kano domin fuskantar shari’a kan manyan laifuka da suka hada da: hada baki don tada rikici, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, tsoratarwa, lalata kayan zabe, satar akwatin kuri’a, da neman kuri’ar mutane a ranar zabe.

Kwamishinan ya jinjinawa hadin gwiwar jami’an tsaro a karkashin ICCES bisa jajircewa wajen kare lafiyar jama’a da hana rikicin ya bazu. Ya kuma bukaci jama’ar Kano su kasance masu bin doka da kuma bayar da hadin kai ga jami’an tsaro.

Ya ce, “Tsaron dimokuradiyya aikin kowa ne. Duk wanda ya ga wani abin da bai dace ba, ya gaggauta sanar da jami’an tsaro ta wayoyinmu na gaggawa.”

Rundunar ta fitar da lambobin da jama’a za su iya kira idan akwai matsalar tsaro: 08032419754, 08123821575, 09029292926.

Leave a Reply