Rundunar ‘yansandan Kano ta kama mutane 98 da ake zargi da laifuka tare da kayayyakin laifukan

0
166
Rundunar 'yansandan Kano ta kama mutane 98 da ake zargi da laifuka tare da kayayyakin laifukan
Kwamishinan 'yansandan Kano

Rundunar ‘yansandan Kano ta kama mutane 98 da ake zargi da laifuka tare da kayayyakin laifukan

Daga Jameel Lawan Yakasai

Rundunar ’yansandan Jihar Kano ta bayyana kama mutane 98 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban tare da gabatar da su a gaban manema labarai, sannan ta nuna wasu kayayyakin da aka samu nasarar kwato su a hannunsu.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya jagoranci holen a ranar Alhamis, 10 ga Yulin 2025, shalkwatar rundunar da ke Bompai.


KU KUMA KARANTA: Rundunar ‘yansandan Kano ta kama mutane 4 da ake zargi da kai hari gidan Sarkin Kano Sanusi II

Yace cikin waɗanda aka kama akwai mutum 21 da ake zargi da garkuwa da mutane, mutune 12 satar mota, mutane 8 zargin sata shanu, mutane 4 ana zarginsu da fyaɗe, mutane 5 da ake zargi da safarar makamai, sai kuma mutane 47 da ake zargi da zama ’yan daba.

Kazalika, rundunar ta bayyana wasu muhimman kayayyakin da ta kama da suka haɗa da motoci guda 6, babura 8, bindigogi na gida 13, wuƙake 98, tabar wiwi guda 35 da ƙananan dauri guda 1,123, ƙwayoyi masu haɗari irin su Madarar Suck and Die, Kwayar Exol, D5, da Diazepam fiye da guda 150, da kuma kuɗin ƙasar waje har Dala $10,000.

Kwamishinan ya ce nasarorin sun biyo bayan sabbin dabarun da rundunar ke amfani da su karkashin shirin Operation Kukan Kura, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomi da al’umma.

Ya buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa ’yan sanda haɗin kai da bayar da bayanan sirri domin ci gaba da yakar miyagun laifuka a jihar.

Leave a Reply