Rundunar ‘yansandan Kano ta kama mutane 4 da ake zargi da kai hari gidan Sarkin Kano Sanusi II
Daga Jameel Lawan Yakasai
Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta kama wasu mutane hudu da ake zargi da kai hari gidan Sarkin Kano na 16 Malam Muhammadu Sanusi na II dake kofar kudu a ranar Lahadi.
Mai magana da yawun rundunar ‘Yan sandan Kano, SP Abdullahi ya tabbatarwa da manema labarai hakan ta cikin wani sakon WhatsApp da ya aike a yau Talata.
A cewar Kiyawa sun kama mutane hudu kuma suna ci gaba da gudanar da bincike a kansu.
KU KUMA KARANTA: ‘Yansanda a Kano za su yi binkice kan matashin da ya hau ƙarfen tallace-tallace
Ranar Lahadin da ta gabata bangaren masarautar Kano sukai zargin tawagar tsohon sarki Kano Aminu Ado Bayero sun kai musu hari, da barnatar da dukiya.









