Rundunar ‘yansandan Kano ta kafa kwamitin binciken rikicin da ya ɓarke tsakanin magoya bayan Sarki Aminu Ado da Sarki Sanusi II

0
335
Rundunar 'yansandan Kano ta kafa kwamitin binciken rikicin da ya ɓarke tsakanin magoya bayan Sarki Aminu Ado da Sarki Sanusi II
Sarki Sanusi II da Sarki Aminu Ado

Rundunar ‘yansandan Kano ta kafa kwamitin binciken rikicin da ya ɓarke tsakanin magoya bayan Sarki Aminu Ado da Sarki Sanusi II

Daga Jameel Lawan Yakasai

Rundunar yansanda ta kafa wani kwamitin mutum takwas domin bincikar rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da na Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.

Kwamishinan yansandan Kano, Ibrahim Bakori ne ya sanar da haka a daren Laraba, yayin da yake karɓar bakuncin sabbin shugabannin kungiyar wakilan kafafen yada ta kasa reshen Kano waɗanda suka kai masa ziyara.

Ya ce kwamitin na da aiki na gano musabbabin rikicin domin gano waɗanda ke da hannu da kuma ba da shawarwari kan matakan da ya kamata a ɗauka.

Ya ƙara da cewa, an kaddamar da kwamitin ne a ranar Litinin, kuma ana sa ran zai mika rahotonsa cikin kwana bakwai 7.

Rikicin dai ya faru ne a ranar Lahadi a fadar Kofar Kudu, lokacin da sarki Aminu ke komawa fadar Nassarawa bayan ziyarar ta’aziyya da ya kaiwa iyalan marigayi, Alhaji Aminu Alhassan Dantata.

Leave a Reply