Rundunar ‘yansandan Kano ta ƙwato motar wani jami’in sojin sama da aka yi wa fashi

0
222

Rundunar ‘yansandan Kano ta ƙwato motar wani jami’in sojin sama da aka yi wa fashi

Daga Jameel Lawan Yakasai

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a ranar Laraba 29 ga Oktoba 2025.

Sanarwar ta bayyana cewa, wasu ƴan fashi sun shiga wani gida da ke Karu a Abuja, inda suka sace kuɗi, wayoyi da motar Ford Escape mallakar wani jami’in Sojin Sama.

Bayan samun bayanan sirri cewa masu laifin sun kamo hanyar zuwa Kano, rundunar ta tura tawagar yaki da satar mutane wadda ta tare motar a kan hanyar Kano zuwa Zaria, kusa da gidan man Salbas.

KU KUMA KARANTA: ‘Yansanda a Kano sun cafke riƙaƙƙen ɗan daba Mu’azu Barga 

Sanarwar ta ce lokacin da jami’an suka yi ƙoƙarin tare masu laifin, sun bude musu wuta, amma an cafke mutane biyu da ake zargi da hannu a lamarin, waɗanda suka haɗa da Adamu Adam Abubakar na Zoo Road a Kano da Umar Bello na Nasarawa Dirkania a Jihar Kaduna, yayin da wani mai suna Dan Malam ya tsere da bindiga da wasu kayan da aka sace.

Sanarwar ta ƙara da cewa ƴan sanda na ci gaba da bin diddigin wanda ya tsere tare da kira ga jama’a da su ci gaba da ba da bayanai ga rundunar don tabbatar da tsaro a jihar.

Leave a Reply