No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar ‘yansandan Kano sun haramtawa ƙanana yara tuƙa baburan Adaidaita sahu a jihar

Daga Jameel Lawan Yakasai

Rundunar ’yansanda ta jihar Kano ta bayyana damuwa kan yadda ake samun ƙananan yara na tuƙa Adaidaita Sahu a cikin birnin Kano, lamarin da ta ce ya janyo haɗura guda 16 a watan Agusta, 2025, tare da jikkata mutane da lalata dukiyoyi.

Jaridar Neptune Prime ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a madadin Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori.

KU KUMA KARANTA: An hana ‘yan adaidaita sahu bin manyan tituna a Kano

Rundunar ta tunatar da cewa hana ƙananan yara tuka Adaidaita Sahu ya zama dole ne domin guje wa haɗura.

Ta yi gargaɗin cewa iyaye da mamallaka baburan za su fuskanci hukunci idan aka kama ’ya’yansu ƙanana suna tuka Adaidaitar.

Rundunar ta kuma gargadi dukkan masu ababen hawa da su kiyaye dokokin zirga-zirga, tare da jan hankalin cewa za a cafke kuma a gurfanar da masu karya doka a kotu.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...