Rundunar ‘yansanda ta ba da umarnin bincike kan mutuwar ma’aikaciyar gidan talabijin na Arise

0
108
Rundunar 'yansanda ta ba da umarnin bincike kan mutuwar ma’aikaciyar gidan talabijin na Arise
Marigayiya Somtochukwu, wakiliyar gidan Talabijin ta Arise

Rundunar ‘yansanda ta ba da umarnin bincike kan mutuwar ma’aikaciyar gidan talabijin na Arise

Rundunar ’Yansanda ta Babban Birnin Tarayya, Abuja, ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan yanayin da ya haifar da rasuwar mai gabatar da shirye-shirye ta gidan talabijin na Arise, Somtochukwu Maduagwu.

Jami’ar hulɗa da jama’a ta ’yansanda a Abuja, SP Josephine Adeh ce ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata a Abuja.

Adeh ta ce marigayiyar ta rasa ranta cikin mummunan hali sakamakon harin ’yan fashi da makami a gidanta da ke unguwar Katampe a Abuja da safiyar Litinin.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya raba wa ‘yan jarida 100 kwamfuta, ya yi kira da a yi ingantaccen rahoto

Ta ce kwamishinan ’yansanda na Abuja, Ajao Adewale, ya bayyana lamarin a matsayin mugun aiki marar ma’ana da bai dace da kowace al’umma mai mutunci ba.

“A bisa haka ne, CP ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi da tsanaki kan yanayin da ya haifar da wannan lamari.

“Haka kuma, ya bada umarnin tura jami’an leken asiri da na aikin tsaro domin ganowa da bin sawu da kuma cafke wadanda ke da alhakin wannan mummunan laifi,” in ji ta.

Adeh ta yi alkawarin cewa za a tabbatar da adalci a wannan lamari tare da tabbatar da jajircewar rundunar wajen kare lafiyar jama’a da kuma hana faruwar irin wannan abu a nan gaba.

Ta roki jama’a da su tallafa wa binciken da ake yi ta hanyar samar da bayanai cikin lokaci da za su taimaka wa ’yan sanda.

Adeh ta kuma ja hankalin jama’a da su rika daukar matakin gaggawa a duk lokacin da suka lura da abin da ke da ban shakku domin hana masu aikata laifi damar aiwatar da mugayen shirin su.

Leave a Reply