Rundunar ‘yansanda a Yobe ta kama wata mata da ake zargi ta kashe mijinta, sakamakon rikici a kan abinci

0
159
Rundunar 'yansanda a Yobe ta kama wata mata da ta kashe mijinta, sakamakon rikici a kan abinci

Rundunar ‘yansanda a Yobe ta kama wata mata da ake zargi ta kashe mijinta, sakamakon rikici a kan abinci

Rundunar ‘yansandan jihar Yobe ta kama wata mata mai suna Hadiza Mamuda ‘yar shekara 35 bisa zargin kashe mijinta a wani rikici da ya ɓarke a cikin gida a kan abinci.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Garin Abba da ke ƙaramar hukumar Fika a jihar.

Shaidu sun tabbatar da cewa wadda ake zargin ta buga wa mijin nata itace ne a lokacin da suke taƙaddama a tsakar kansa, wanda ya kai ga mutuwarsa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce wanda aka kashen yana da mata biyu da ‘ya’ya biyar, ɗaya daga cikin matan nasa ita ce wanda ake tuhuma kashe shi.

KU KUMA KARANTA: ‘Yansanda a Jigawa sun kama magidanci ɗan shekara 70 kan zarginsa da kashe ‘yar’uwarsa 

Ya ƙara da cewa ana gudanar da bincike kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda (PPRO) ya bayyana cewa, kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Emmanuel Ado, ya bayyana faruwar lamarin a matsayin abin ban tausayi, ya kuma jaddada muhimmancin wayar da kan al’umma don magance tashe-tashen hankula da rikici a tsakanin ma’aurata a cikin gida. Ya yi ƙira ga shugabannin addini da na al’umma da su ƙara wayar da kan jama’a kan illolin da ke tattare da cin rikici a tsakanin ma’aurata.

Leave a Reply