Rundunar ‘yansanda a Kano, ta kama ‘yansandan bogi

0
142
Rundunar 'yansanda a Kano, ta kama 'yansandan bogi

Rundunar ‘yansanda a Kano, ta kama ‘yansandan bogi

Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce jami’anta sun kama ƴansandan bogi uku da ake zargi da yin damfara ta hanyar shigar burtu a matsayin ƴansanda a jihar Kano, bayan sun damfari wani mutum naira miliyan ɗaya da dubu talatin.

BBC Hausa ta rawaito cewa mutanen da aka kama sun fito ne daga ƙaramar hukumar Daura ta jihar Katsina inda aka kama su a ranar 2 ga Satumba, 2025, a Danagundi Quarters.

Rundunar ce ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da Jama’a na ƴansanda, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar.

Sanarwar ta ce “Kamar yadda bincike ya nuna, an kama su ne bayan wanda suka damfara ya nemi ɗauki, inda ya yi bayanin yadda abin ya faru.

KU KUMA KARANTA:‘Yansanda a Kano sun cafke riƙaƙƙen ɗan daba Mu’azu Barga 

“Binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargi sun yi shigar burtu a matsayin ƴansanda inda suka yi iƙirarin cewa suna da wasu ƙwarewa na musamman da za su taimaka wa wanda aka damfara kuma suka umurce shi ya kai kudin wani wuri,” in ji sanarwar.

Daga nan ne jami’an ‘yansanda suka gaggauta ɗaukar mataki tare da haɗin gwiwar jama’a, wanda ya haifar da kama wadanda ake zargin.

Ana ci gaba da gudanar da bincike, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala binciken.

Leave a Reply