Rundunar ‘yan sandan Najeriya sun hana faɗin sabuwar sarar ‘No Gree For Anybody’

0
189

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gargaɗi ‘yan Najeriya da ka da su yi amfani da wata sabuwar sara da ta fito, “No dey gree for anybody”

Kakakin rundunar ‘yan sandan, ACP Muyiwa Adejobi, ne ya yi wannan gargaɗin yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Abuja a ranar Laraba.

Ya ce, “Sabuwar sarar ta 2024 ga matasan mu ita ce; “No dey gree for anybody.”

“A cewar bayanan sirrinmu, taken yana fitowa ne daga wani ɓangare na juyin juya hali wanda zai iya haifar da matsaloli a faɗin ƙasar.

“Babu yarda ga kowa” ana ɗaukarsa a zaman wata sara, amma a cikin duniyar tsaro, muna kallonsa a matsayin kalma mai haɗari wacce zai iya haifar da rikici.”

Leave a Reply