Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama mutane 49 da ake zargi da sata a Triumph Plaza Kano

1
630

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama mutane 49 da ake zargi da sata a shagunan kasuwanci dake Triumph a ƙaramar Hukumar Fagge dake jihar Kano.

Hakan na ɗauke cikin wata sanarwar manema labarai da Kakakin Rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Litinin.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kama mutane biyu da laifin daɓa wa matashi wuƙa, ya mutu har lahira

“A ranar Lahadin da ta gabata da misalin ƙarfe 10 na dare, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu rahoton cewa wasu ɓata gari sun yi ayari sun nufi unguwar Fagge dan yin satar kayayyakin mutane a Triumph Plaza.” Inji Sanarwar.

“Da samun wannan rahoto kwamishinan ‘yan Sanda CP Mohammed Usaini Gumel ya bada umarni ga dakarun ‘yan sanda na Operation ‘Restore Peace’ inda suka yi nasarar fatattakar ɓarayin. An kuma yi nasarar kama 49 daga cikin su tare da ceto wasu kayayyaki da suka sata.”

“Daga kayan da aka yi nasarar ceto wa, akwai ƙofofin alfarma guda 3, tagogi, Na’urar sanyaya ɗaki guda 4, ƙarafunan ƙofa guda 8, da kuma manyan guduma ta fasa gini guda 16.” Inji sanarwar

Rundunar tace ana ci gaba da gudanar da bincike, ta kuma ja hankalin iyaye da jagororin al’umma da su tsawatarwa yaran su da gujewa satar kayan mutane.

A kwanakin nan an samu yawaitar satar kayan mutane a wuraren da gwamnatin Jihar Kano ta yi rusau inda matasan ke iƙirarin ganima suke ɗiba.

1 COMMENT

Leave a Reply