Rundunar ’yan sanda ta ba da miliyan 18 ga iyalan jami’anta da suka mutu

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Gombe, Oqua Etim, ya miƙa wa iyalan jami’an rundunar su 25 da suka rasu a bakin aiki zunzurutun kuɗi har Naira miliyan 18 da dubu 500.

Kwamishinan ya ce wannan kuɗi wani tallafi ne daga Babban Sifeton ‘Yan Sandan Najeriya, Alkali Baba Usman da kuma Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda don rage musu raɗaɗin mutuwar iyalai da iyayensu.

A cewarsa, yanzu an zo lokacin da magadan mamatan za su gane cewa iyayensu sun hidimta wa ƙasa ta hanyar aiki da hukumar da za ta share musu hawaye.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kama mutane 7 da suka kashe direban mota

Daga nan sai ya yi kira gare su da su yi amfani da kuɗin ta hanyar da ta dace domin su amfane su.

Wasu iyalan jami’an da suka rasu da suka zanta da manema labarai cikin alhini, Atiku Ibrahim da Ruth Yusuf, sun nuna farin cikin su ga tallafin domin a cewar su, haƙƙoƙin ’yan’uwansu da suke tsammani an riga an biya su, shi kuma wannan wani tallafi ne da basu san da shi ba.

Sun kuma ƙara gode wa hukumar da Kwamishinan ’Yan sandan jihar bisa wannan tagomashin da aka musu.


Comments

One response to “Rundunar ’yan sanda ta ba da miliyan 18 ga iyalan jami’anta da suka mutu”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Rundunar ’yan sanda ta ba da miliyan 18 ga iyalan jami’anta da suka mutu […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *