Rundunar ‘yan sanda sun kama mutum 307 a wani samame maɓoyar ɓata-gari a Abuja

0
207

Rundunar ‘yan sanda a Abuja, babban birnin Najeriya ta ce ta kai samame wata matattarar miyagu inda ta kama mutum ɗari uku da bakwai da ake zargi da aikata laifuka.

Kwamishinan ‘yan sanda a Abuja, CP Benneth C. Igwe ne ya jagoranci tawagar rundunar ‘Operation Velvet’ wajen kai samame kan matattarar da ke Gidan Dambe a yankin Dei-Dei zuwa Zuba.

Yayin binciken, an gano bindiga ɗaya da alburusai goma sha biyar a hannun wani da yake iƙirarin shi jami’in hukumar tsaro ta farin kaya ne.

A cewar sanarwar da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta wallafa a shafin X, sauran kayayyakin da aka gano sun hada da babura da ƙunshin tabar wiwi da haramtattun ƙwayoyi da ake zargi mutanen sun sace ne daga hannun mutanen da ba su ji ba su gani ba.

KU KUMA KARANTA: Ƴan sanda a Bauchi sun bankaɗo bindigogin AK-47 da miliyan 4.5 a maɓoyar masu garkuwa da mutane

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan mutanen da aka kama.

A makon da ya gabata ne aka ƙaddamar da rundunar ta musamman domin kawo ƙarshen duk wasu miyagun laifuka a Abujar.

Kwamishinan ya kuma gargaɗi ‘yan sanda kan tatsar jama’ar sannan su nuna ƙwarewa wajen aiwatar da ayyukansu.

Leave a Reply