Dubun wasu matasa uku da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama da wayoyin hannu 318 waɗanda ake zargin na sata ne ta cika.
Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta ranar Asabar.
Kiyawa ya bayyana cewa tun da farko wani mai suna Muhammad Adam da wasu mutane 9 ne suka kai musu ƙorafi kan cewa da tsakar dare ɓarayi sun fasa musu shaguna a kusa da filin wasa na Sani Abacha dake ƙofar Mata Kano, inda suka sace wayoyi 671.
Nan take ‘yan sanda suka soma bincike wanda har ya kai ga kama mutanen uku, sun kuma amsa laifin da ake zargin su da aikata wa.
KU KUMA KARANTA: An kama ɓarayin da suka fasa shago suka saci wayoyin hannu 996 da kwamfuta tara
Sai dai waɗanda ake zargin sun shaida wa ‘yan sandan cewa tuni suka sayar da wasu daga cikin wayoyin.
SP Kiyawa ya bayyana cewa za a gurfanar da mutunen a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.