No menu items!

Sample Page Title

Date:

Hedikwatar rundunar mayaƙan ruwan Najeriya ta gano masu yi mata sojan gona a matsayin sojojin ruwa.

Kakakin mayaƙan ruwan Najeriya, Navy Commodore Ayo Vaughan ya shaida wa VOA Hausa cewa su waɗannan sojojin ruwan bogi da aka gano na da hedikwatarsu a shiyyar kudu maso kudancin Najeriya ne, inda suke gudanar da haramtacciyar hada-hadarsu.

Za ka gansu tsaf-tsaf cikin kakin sojojin ruwa maƙale da lambobin girma da ababen dai da ke jikin kakin sojin ruwan har ma wani babban ofis suke da shi da adireshin yanar gizo, har ma sai da form na ɗaukar aiki su ke yi inda suke damfarar jama’a.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun sake ceto ɗaya daga cikin ‘yan matan Chiɓok

Wannan rundunar mayaƙan na bogi na nuna izza da isa yayin da a wani lokaci suke cin zalin jama’a a matsayin su sojoji ne.

Saboda haka Hedikwatar mayaƙan Ruwan Najeriya ta ce za ta ɗau mataki mai tsanani akansu kana ta nemi jama’a da su yi taka tsantsan, sannan su kai rahoton duk waɗanda ba su yarda da take-takensu ba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...