Connect with us

Labarai

Rundunar sojin Najeriya tana tuhumar jami’anta kan kisan mutane a Tudun Biri

Published

on

Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce tana tuhumar wasu dakarunta bisa zargin kisan fararen-hula a ƙauyen Tudun Biri na jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar.

Mai magana da yawun hedkwatar, Edward Buba, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da ya gudanar ranar Alhamis a Abuja babban birnin ƙasar.

Edward Buba ya ce an kammala bincike kan sojojin kuma hedkwatar tsaron Najeriya za ta hukunta duk wanda ta samu da laifi a kisan mutanen na Tudun Biri, tare da yi wa ‘yan’uwan waɗanda aka kashe adalci.

“Rundunar soji ta yi cikakken bincike kan lamarin sannan ta soma bin tsarin hukunta waɗanda aka samu da laifi. Don haka, waɗanda ke da hannu a wannan lamari za su fuskanci hukunci daga kotun soji. Ba na so na yi maganar da ta wuce wannan,” in ji shi.

KU KUMA KARANTA: Za mu hukunta masu hannu a harin Tudun Biri — Hafsan Tsaro

A ranar 3 ga watan Disamba ne wani jirgi maras matuƙi na rundunar sojojin Najeriya ya kai hari a kan wasu mutane da ke bikin Maulidi a ƙauyen Tudun Biri inda sojojin ƙasar suka ce an kai harin ne a bisa kuskure.

Harin ya yi sanadin mutuwar fararen-hula kusan 100 kuma ya jawo kakkausan suka daga cikin da wajen Najeriya. A wancan lokacin, shugaban ƙasar Bola Tinubu ya lashi takobin gudanar da bincike mai tsauri kan lamarin tare da hukunta waɗanda ke da laifi.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Iftila'i

Ruwan sama ya yi ajalin mutum 3, da lalata gidaje a Yobe

Published

on

Ruwan sama ya yi ajalin mutum 3, da lalata gidaje a Yobe

Ruwan sama ya yi ajalin mutum 3, da lalata gidaje a Yobe

Aƙalla mutum uku sun rasu, yayin da wasu bakwai suka jikkata, bayan da wani gini ya rufta sakamakon mamakon ruwan sama a ƙaramar hukumar Nangere da ke Jihar Yobe.

Iftila’in ya faru ne a Tsohon Gari da ke hedikwatar ƙaramar hukumar Nangere a ƙarshen wannan makon.

Majiya daga yankin ta ce sama da gidaje 50 ne suka lalace, lamarin da ya sanya mutane da dama rasa matsugunansu.

Wani mazaunin yankin, Shuwa Adamu, ya shaida wa Aminiya cewar ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da iska ne ya yi sanadin rushe gidajen.

“Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 9 na safe lokacin da yawancin mazauna yankin ke shirin fita kasuwa kamar kullum.

KU KUMA KARANTA: Ruwan sama ya lalata gidaje da gonaki a jihar Kogi

“Akalla shaguna da gidaje 50 ne suka lalace, sai kuma wani yaro ɗan shekara bakwai da ya rasu.
“Jami’an Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe sun tantance adadin asarar da aka yi a yankin,” in ji shi.

Wata mazauniyar yankin, mai suna Halima ta ce ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya yi ajalin mutum uku tare da lalata kadarori da dama.

“Sama da gidaje 50 ne suka lalace yayin da mutum uku ciki har da wani yaro ɗan shekara bakwai, suka mutu.
“Mutanen da suka rasa gidajensu a halin yanzu suna tare da danginsu,” in ji ta.

Da yake mayar da martani kan lamarin, sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (Yosema) Dokta Goje Muhammad, ya jajanta wa wadanda abin ya shafa.

Ya ce hukumar ta biya kuɗin kula da lafiyar waɗanda suka jikkata da ke babban asibitin Nangere.

Kazalika, ya ce an sallami waɗanda suka jikkata baki ɗaya daga asibitin.

Continue Reading

Labarai

Tinubu ya naɗa sabbin sakatarorin dindindin

Published

on

Tinubu ya naɗa sabbin sakatarorin dindindin

 

Tinubu ya naɗa sabbin sakatarorin dindindin

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da naɗin sabbin sakatarorin dindindin na gwamnatin tarayya guda takwas da za su cike guraben da ake da su a wasu jihohi da shiyyoyin ƙasar a ma’aikatan gwamnati.

Ajuri Ngelale, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da bayanai ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a jiya Juma’a, inda ya ce an naɗa sabbin sakatarorin dindindin ɗin ne bayan da ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ya gudanar da aikin zaɓo su.

KU KUMA KARANTA:Tinubu ya amince da raba Naira dubu 50 ga iyalai miliyan 3.6 na tsawon watanni 3

Sakatarorin su ne: Dr Emanso Umobong Okop – Akwa-Ibom, Obi Emeka Vitalis – Anambra, Mahmood Fatima Sugra Tabi’a – Bauchi, Danjuma Mohammed Sanusi – Jigawa, Olusanya Olubunmi – Ondo, Dr Keshinro Maryam Ismaila – Zamfara, Akujobi Chinyere Ijeoma (Kudu-maso-Gabas)) da kuma Isokpunwu Christopher Osaruwamwen (Kudu-maso-Kudu).

“Shugaban ya yi hasashen cewa sabbin sakatarorin dindindin na gwamnatin tarayya za su yi aiki da ƙwazo, himma da riƙon amana ga ƙasa wajen gudanar da ayyukansu tare da tabbatar da ingantacciyar hidima ga al’ummar Najeriya,” in ji sanarwar.

Continue Reading

Labarai

Tinubu ya amince da raba Naira dubu 50 ga iyalai miliyan 3.6 na tsawon watanni 3

Published

on

Tinubu ya amince da raba Naira dubu 50 ga iyalai miliyan 3.6 na tsawon watanni 3

 

Tinubu ya amince da raba Naira dubu 50 ga iyalai miliyan 3.6 na tsawon watanni 3

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ba da Naira dubu hamsin-hamsin ga iyalai miliyan 3.6 har tsawon wata uku a faɗin Nijeriya.

Wannan na ɗaya daga cikin yarjejeniyoyi da aka cimma a ganawar da Tinubu ya yi da gwamnonin jihohi 36 na ƙasar nan a yau Alhamis a Abuja.

Shugaban ya ba da umarnin raba kuɗin ga iyalai dubu 100 a kowace jiha har na tsawon watanni uku.

Sauran batutuwa da aka cimma a ganawar sun haɗa da:

* Bawa iyalai 100,000 a kowace jiha tallafin N50,000 na tsahon wata uku.

* Ware Naira biliyan 155 domin siyen kayan abinci da za a tallafawa masu ƙaramin ƙarfi kan farashi mai rahusa.

* Baiwa kowace jiha Naira biliyan 10 domin sayen motocin sufuri masu aiki da iska gas domin sauko da farashin kuɗin zirga-zirga.

KU KUMA KARANTA:Tinubu ya jajantawa mutanen da gobarar kasuwar Karu ta shafa

* Gaggauta fara aikin hanyar da ta tashi daga Sakkwato zuwa Badagary a Lagos. Hanyar zata ratsa ƙauyuka kimanin 216, madatsun ruwa (dams) guda 58, ƙananan hukumomi 156 da manyan garuruwa 39 da kuma gonaki da suka kai kimanin hectare miliyan ɗaya. Titin zai ratsa jihohin Sokoto da Kebbi da Niger da Kwara da Oyo da Ogun da kuma Lagos.

* Shugaba Tinubu ya kuma amince da biyan kuɗin aikin hanyar jirgin ƙasa daga Fatakwal zuwa Maiduguri wadda za ta ratsa jihohin Rivers da Abia da Enugu da Benue da Nasarawa da Plateau da Bauchi da Gombe da Yobe da kuma Borno.

* Haka nan an amince da biyan kuɗin da ake buƙatar domin yin aikin hanyar jirgin ƙasa da ta taso daga Ibadan zuwa Abuja a wani ɓangare na aikin dogo da ya tashi daga Lagos zuwa Kano. Aikin zai haɗa jihohin Lagos da Ogun da Oyo da Osun da Kwara da Niger da Abuja da Kaduna da kuma Kano.

* Shugaban ƙasa ya kuma bada umarnin cigaba da aikin hanyar Lagos zuwa Calabar wadda kuma zata yi rassa a jihohin Benue da Kogi da Abuja da Nasarawa da Enugu da Ebonyi.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like