Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta gano wasu bama-bamai 9 da basu fashe ba
Daga Shafaatu Dauda Kano
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta gano wasu bama-bamai 9 da ba su fashe ba, a gurin da bom ya fashe kusa da wani kamfanin karafa na Yongxing Steel Company, da ke kan hanyar Ring Road, Mariri, a jihar.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da mataimakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Hussaini Abdullahi, ya fitar a ranar Lahadi 22 ga Yuni, 2025.
Sanarwar ta ce, “Bayan gano bama-bamai 7 da ba su fashe ba a baya, an sake bankado guda biyu, wanda hakan ya kai adadin gaba ɗaya zuwa tara.”
KU KUMA KARANTA: Rundunar ‘Yan Sanda Kano ta kama manyan waɗanda ake zargi da hannu a kisan gillar DPO din Rano, Marigayi CSP Baba Ali
Binciken ‘yan sanda ya gano cewa an haɗa bama-baman da shara, wadda aka kawo daga Jihar Yobe ba tare da an sani ba, kuma ɗaya daga cikinsu ya fashe yayin da ake sauke kayan a filin kamfanin.
Rundunar ta roƙi al’umma da su kwantar da hankula tare da kira ga jama’a da su ci gaba da sanar da hukumomi idan sun ga wani abu da ya daure musu kai.
Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu guda biyar, tare da yi wa waɗanda ke jinya a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano fatan samun sauƙi cikin gaggawa.









