No menu items!

Sample Page Title

Date:

Tawagar ƙarshe ta sojojin Faransa za ta kammala ficewa daga Jamhuriyar Nijar a yau Juma’a, abin da ya kawo ƙarshen fiye da shekaru goma da suka kwashe suna yaƙi da masu iƙirarin jihadi a ƙasar.

Ficewar dakarun Farana ta bar ɗaruruwan sojojin Amurka da gomman sojojin Italiya da na Jamus a ƙasar ta Nijar.

Faransa ta ce za ta kwashe dakarunta kusan 1,500 da suka haɗa da matuƙan jiragen yaƙi daga Nijar bayan dangantaka ta yi tsami tsakaninta da sojoin ƙasar wadanda suka kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum a watan Yulin da ya gabata.

Wannan ne karo na uku cikin watanni 18 da aka kori dakarun Faransa daga wata ƙasa a yankin Sahel.

KU KUMA KARANTA: Rundunar sojin Faransa za ta fara kwashe dakarunta daga a jamhuriyar Nijar

An tilasta musu ficewa daga Mali da Burkina Faso a farkon wannan shekarar bayan sojoji sun yi juyin mulki a kasashen biyu.

Dukkan kasashen uku suna yaki da kungiyoyi masu ikirarin jihadi wadanda suka kaddamar da hare-hare a arewacin Mali a 2012, sannan daga bisani suka shiga Nijar da Burkina Faso.

Jerin juye-juyen mulkin da aka yi a yankin tun daga 2020 ya sanya dangantaka ta yi tsami tsakanin Faransa da kasashe da ta yi wa mulkin mallaka, abin da ya bai wa Rasha damar yaukaka dangantaka tsakaninsu.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...