Rukunin farko na Alhazan Kano sun tashi zuwa Saudiyya

1
285
Rukunin farko na Alhazan Kano sun tashi zuwa Saudiyya
Mahajjata

Rukunin farko na Alhazan Kano sun tashi zuwa Saudiyya

A yau Litinin ne kimanin maniyyata 505 daga Jihar Kano suka tashi zuwa ƙasar Saudiyya don sauƙe farali a shirye shiryen da ake yi na Hajjin bana.

Maniyyatan wanda su ne rukunin farko sun tashi daga filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu Kano da misalin ƙarfe 11:30 na safe a cikin jirgin Max Air.

Ana sa rai maniyyatan za su sauƙa a Filin sauka da tashi na King Bn Abdulazeez da ke Jidda.

A jawabinsa na ban kwana, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi ƙira ga alhazan da su zama wakilai na gari ga jihar da ma ƙasar gaba daya, inda ya kuma yi kira gare su da su yi wa kasar addu’a don samun cikakken zaman lafiya da karuwar arziki.

Gwamnan ya kuma gargaɗi alhazan da su guji sanya kansu cikin harkokin tu’ammali da miyagun kwayoyi ko yin sata da sauran abubuwa marasa kyau don guje wa fuskantar hukunci mai tsanani daga ƙasar ta Saudiyya.

KU KUMA KARANTA: Hukumar Alhazan Najeriya NAHCON ta ƙara kuɗin kujerar aikin Hajjin 2024

A jawabinsa tunda farko, Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Laminu Danbappa, ya bayyana cewa rukunin farko na alhazan sun fito daga ne kananan hukumomin Dala da Fagge da Gwale da Ungogo.

Dambappa ya yi ƙira ga alhazan da su kula da kudin guzurinsu tare da kashe su ta hanyar da ta dace.

Maniyyata 3,121 ne daga Jihar Kano ake sa rai za su sauke farali a bana.

1 COMMENT

Leave a Reply