No menu items!

Sample Page Title

Date:

Christiano Ronaldo ya ce har yanzu akwai sauran ƙwallayen da zai ci a bana bayan ya ci kwallonsa ta 50 a 2023.

Ya bayyana haka ne bayan ƙungiyarsa ta Al Nassr ta ci Al Shabab 5-2 a gasar Cin Kofin Sarkin Saudiyya.

Tsohon ɗan wasan na Manchester United da Real Madrid ya ci ƙwallon a kusa da kusa da kafarsa ta dama a minti na 74.

“Babban nasara kuma ina farin cikin sanar da cin kwallota ta 50 a 2023,” kamar yadda ɗan wasan na Portugal mai shekara 38 ya rubuta a shafinsa na Instagram bayan ƙwallon tasa ta taimaka wa kulob ɗin ya kai zagayen kusa da na ƙarshe a ranar Litinin.

“Ina godiya da irin goyon bayan da na samu daga ‘yan ƙungiyata da magoya bayana da kuma iyalina! Akwai sauran damar cin wasu a bana.”

Ɗan wasan ya ci aƙalla ƙwallo ɗaya a kusan duka wasan da ya buga wa ƙungiyar ta Al Nassr. Haka kuma ya ci ƙwallon goma ga Portugal a wasanni tara da ya buga a 2023.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...