Daga Ibraheem El-Tafseer
A watan Janairu Ronaldo ya koma taka-leda a Saudiyya, bayan raba gari da Manchester United.
Cristiano Ronaldo ya ɗauki kofin Zakarun ƙasashen Larabawa bayan da ƙungiyarsa ta Al-Nassr ta doke Al-Hilal da ci 2-1.
Ɗan wasan na ƙasar Portugal ne ya zura duka ƙwallo biyun da ƙungiyar ta ci a ƙarawar.
Wannan shi ne kofi na farko da Ronaldo ya ci tun bayan komawa ƙungiyar a watanni takwas da suka gabata.
Bayan kammala gasar Kofin Duniya ne, Ronaldo ya koma taka-leda a Saudiyya, bayan raba gari da ƙungiyarsa ta Manchester United.
Komawar tsohon ɗan wasan Real Madrid ɗin zuwa Saudiyya ta buɗe ƙofa ga sauran fitattun ‘yan wasan Turai wajen komawa buga gasar ta Saudiyya.
KU KUMA KARANTA: Ba za a manta da Pele ba, in ji hukumar kwallon kafa ta FIFA
Cikin wannan shekara fitattun ‘yan wasa irin su Karim Benzema da Ngolo Kante da Riyad Mahrez da sauran ‘yan wasan Turai da dama ne suka koma buga gasar ta Saudiyya.