Rikicin ruwa yana haifar da rikice-rikice a duniya – Shugaba Erdogan

0
39

Rikicin ruwa yana haifar da rikice-rikice a duniya – Shugaba Erdogan

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yi kira da a mayar da hankali kan yadda rikicin ruwa ke ƙara taɓarɓarewa a duniya.

“Yawancin rikice-rikice a Asiya da Amurka da Arewacin Afirka, da kuma Gabas ta Tsakiya sun samo asali ne daga taƙaddamar hanyoyin ruwa,” in ji Erdogan a ranar Juma’a a jawabin da ya yi a wani taron albarkatun noma da Bankin Ziraat na kasar Turkiyya ya shirya a Istanbul.

Ya ƙara da cewa, “Sakamakon illar da sauyin yanayi ke haifarwa, hanyoyin ruwa da wuraren da tafkuna suke suna zama wuraren da ake fama da rikici.”

KU KUMA KARANTA: Turkiyya ce ta aika da kayan agaji  mafi yawa zuwa Gaza da ya kai tan 50,000 — Erdogan

Erdogan ya kuma taɓo batun cinikin hatsin da Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya suka ƙulla tsakanin Rasha da Ukraine a shekarar 2022.

“Idan ba don yarjejeniyar cinikin hatsin da Turkiyya ke jagoranta ba, da da yawa yankunan sun yi fama da yunwa musamman ƙasashen Afirka,” in ji shi.

Shugaban ya jaddada cewa Turkiyya “ta hana lamarin yin muni ta hanyar tabbatar da wucewar tan miliyan 33 na hatsi ta cikin mawuyacin hali” a cikin bala’in cutar ta Covid-19 da yakin Ukraine.

Leave a Reply