Connect with us

Labarai

Rikicin manoma da makiyaya ya yi ajalin mutum 12 a Taraba

Published

on

Wani rikici da ya ɓarke tsakanin makiyaya da manoma ya yi ajalin manoma 10 da makiyaya 2 a ƙauyen Jenuwa na ƙaramar hukumar Takum a jihar Taraba.

Rahotanni sun nuna an kashe manoman ne waɗanda dukkansu ’yan uwan juna ne lokacin da suke hanyarsu ta zuwa gona domin yin girbi a ranar Juma’a.

Aminiya ta gano cewa an yi wa manoma kwanton-ɓauna ne a kusa da gonar tasu.

Shugaban ƙungiyar ’yan ƙabilar Kutep na Kasa, Emmanuel Ukwen ya shaida wa Aminiya cewa dukkan manoman da aka kashe ’yan ƙabilarsu ne.

KU KUMA KARANTA: An jikkata mutane da dama a rikicin makiyaya da manoma a Kano

Ya kuma zargin cewa ’yan kwanakin kafin wannan harin, makiyayan sun kuma kai musu hari inda suka kashe matasa biyu, sannan suka yi wa wata mata fyaɗe.

Ya ce bayan haka ne su ma suka ƙaddamar da harin ramuwar gayya, inda suka kashe makiyaya biyu, suka raunata wasu biyu.

Emmanuel ya kuma yi zargin cewa bayan waccan ramuwar gayyar ce shi ne makiyayan suka kuma dawowa suka kashe musu mutum 10 a ranar Juma’a

Sai dai a cewar shugaban ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti-Allah, reshen Kudancin Taraba, Ya’u Ibrahim Barewa, matasa sun tare mutanensu huɗu da ke kan hanyar Takum zuwa Kashinbila, inda suka kashe biyu daga ciki, suka kuma raunata biyun.

Ya kuma ce an matasan sun kashe musu shanu 15, amma ya ce yana da wahala a iya tantance ainihin wanda ya kashe manoma 10, tun da babu wanda aka kama.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Usman Abdullahi ya tabbatar da kisan manoman guda 10.

Ya kuma ce, “Ofishinmu da ke Takum ya aiko wa hedkwatar rundunarmu rahoton cewa wasu mahara da ba a san ko su wane ne ba sun kashe manoma 10 a ƙauyen Jenuwa Gida.”

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like