Rikici tsakanin ƙauyukan Osun ya sa an harbi DPO da wasu ’yan sanda huɗu

Wani sabon rikici a kan jayayyar filaye ya sake ɓarkewa a tsakanin al’ummomin garuruwan Ilobu da Ifon da ke maƙwabtaka da juna a Jihar Osun.

An fara rikicin ne cikin daren Laraba zuwa wayewar garin Alhamis.

Wata majiya ta ce mutum ɗaya ya rasa ransa a wajen rikicin sannan an yi ƙone-ƙonen gidaje da kadarori kafin gamayyar jami’an tsaro su shawo kan lamarin.

Wasu majiyoyi a yankin sun shaida wa Aminiya cewa an ga ɗimbin mutane maza da mata suna ƙoƙarin ƙauracewa garuruwan.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Bauchi za ta sasanta rikicin kan iyaka da Jigawa

Da take tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Laraba, Kakakin Rundunar ’Yan Sanda a Jihar, Yemisi Opalola ta ce an yi wa jami’an ’yan sandan da aka tura su kwantar da rikicin kwanton ɓauna da aka harbi babban jami’i (DPO) da jami’ansa 4 tare da ƙona sabuwar motar sintiri a lokacin rikicin.

Kakakin ’yan sandan ta ce duk da yake an shawo kan lamarin sai dai har zuwa lokacin rubuta wannan labari waɗannan jami’an ’yan sanda suna kwance a asibiti da likitoci suke ƙoƙarin ceton rayukansu.

A wani labarin kuma, Gwamnan Jihar, Ademola Adeleke, ya ba jami’an tsaro umarnin harbin duk wanda aka gani yana ƙoƙarin sake tayar da rikici a yankunan.

Gwamnan ya kuma tunatar da mazauna yankin cewa dokar hana fitar da ya sanya har yanzu tana nan daram.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *