Remi Tinubu ta miƙa ɗaliban da aka sace a Jami’ar Dutsin-Ma hannun iyayensu

0
201

Matar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu ta mika ɗalibai mata na Jami’ar tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) da aka sace kwanakin baya hannun iyayensu.

An kuɓutar da ɗaliban ne sakamakon aikin haɗin guiwa tsakanin jami’an tsaro ƙarƙashin kulawar ofishin mai bawa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro (NSA).

Yayin da take karɓar ɗaliban su biyar na jami’ar ta Dutsinma da aka ceto wadanda ‘yan bindiga sukayi garkuwa dasu, Sanata Oluremi ta ce ilimi shi ne babbar hanyar yaƙi da matsalar tsaro a Najeriya.

Sanata Remi Tinubu ta bayyana godiya ga jami’an tsaro da suka yi aikin ceto ƴan matan tare da kira ga ɗaliban da kada su bari abinda ya faru ya kashe musu guiwar neman ilimi.

Mai ɗakin shugaban ƙasar ta kuma bada sanar war tallafin karatu (scholarship) na Naira miliyan 1 ga kowace yarinya a cikinsu da sabuwar kwamfutar tafi-da-gidanka a ƙarƙashin tsarin nan na Renewed Hope Initiative (RHI) da take jagoranta.

KU KUMA KARANTA: Jami’an tsaro sun kama ɗalibi da bindiga a Jami’ar ATBU

Hakazalika, ta sanar da cewa, gwamnatin tarayya ta bayar da kuɗi naira miliyan biyu a matsayin tallafi ga iyayen kowacce daga cikin ‘yan matan da aka ceto.

Waɗannda suka halarci taron miƙa ɗaliban sun haɗa da iyayen ‘yan matan da aka ceto, Mataimakin Shugaban Jami’ar Tarayya Dutsin Ma, Katsina, Wakilin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da wakilin NSA.

Leave a Reply