Remi Tinubu ta fara aiki a matsayin matar shugaban ƙasa

0
488

Oluremi Tinubu, uwargidan shugaban ƙasa Bola Tinibu, a ranar Litinin a Abuja, ta karɓi muƙamin uwargidan shugaban ƙasar Najeriya.

Misis Tinubu da ta isa ɓangaren uwargidan shugaban ƙasa ta samu rakiyar mataimakanta na tsaro.

Uwargidan shugaban ƙasa a lokacin da ta isa wurin, ta samu tarba ne daga babban sakatare na ɓangaren ofishin, Tijjani Umar da sauran shugaban rukunai a ofishin uwargidan shugaban ƙasar.

A don haka aka jagoranci Misis Tinubu rangadin wasu ofisoshi da ke cikin ɓangaren uwargidan shugaban ƙasa, waɗanda suka haɗa da ɓangaren gudanarwa na na’ura mai ƙwaƙwalwa ta zamani (ICT), ɓangaren girke-girke (Catering), yaɗa labarai (Media) da ɓangaren Protocols.

KU KUMA KARANTA: Ya kamata a duba batun ‘mafi ƙarancin albashi’, Tinubu ya gayawa gwamnonin APC

An haifi Misis Tinubu a ranar 21 ga Satumba, 1960, mahaifiyarta Itsekiri, mahaifinta kuma Yoruba.

Ta yi Digiri na farko na Kimiyya a Ilimi daga Jami’ar Ife, kuma ta yi kwasa-kwasai da dama a wasu manyan cibiyoyi.

Ta taɓa zama matar Gwamnan Jihar Legas a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007 sannan aka zaɓe ta a matsayin Sanata mai wakiltar Legas ta tsakiya a Majalisar Dattawa.

Misis Tinubu ta aiwatar da ayyukan jin ƙai da dama domin rage wahalhalun da marasa galihu ke fuskanta a mazabarta.

Leave a Reply