Raɗɗa ya naɗa tsohon mataimakin gwamna a matsayin sakataren gwamnatin jihar

1
273

Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Dikko Raɗɗa, ya naɗa Alhaji Abdullahi Garba tsohon mataimakin gwamnan jihar a matsayin sakataren gwamnatin jihar.

Wannan ya fito ne a wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan, Ibrahim Kaula, ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce Abdullahi ne zai maye gurbin Alhaji Ahmed Ɗangiwa, wanda aka naɗa a matsayin Minista.

Sanarwar wacce aka rabawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Litinin a Katsina, ta ce: “Naɗin zai fara aiki nan take; Ana sa ran Abdullahi zai kawo ɗimbim gogewar da yake da shi a matsayin ‘technocrat’.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Katsina za ta kafa asibitoci 361 – Gwamna Raɗɗa

“Gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jihar da ci gaban al’ummar jihar, a lokacin da yake mataimakin tsohon gwamna Ibrahim Shema, ba ta kai irinsa ba.”

NAN ta ruwaito cewa sabon SSG ya riƙe muƙamin babban lauya kuma kwamishinan shari’a na jihar daga shekarar 2003 zuwa 2009, kafin daga bisani ya koma ma’aikatar ilimi domin yin aiki iri ɗaya.

A halin yanzu shi ne Pro-Chancellor kuma Shugaban Majalisar Gudanarwa na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua ta Katsina.

1 COMMENT

Leave a Reply