Rashin tsaro: Gwamnoni 16 na goyon bayan kafa ‘yan sandan jihohi

0
116

Sakamakon damuwa da taɓarɓarewar matsalar tsaro a Najeriya, gwamnoni 16 sun bayyana goyon bayan kafa ‘yan sandan jihohi.

Majalisar Bunƙasa Tattalin Arziƙin Najeriya ta (NEC) ce ta bayyana hakan a ranar Alhamis a rahoton da aka gabatar mata yayin taronta na 140 wanda ya gudana ta allon gani a ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.

KU KUMA KARANTA:Nijar ta sake buɗe iyakarta da Najeriya

Ministan Kasafi da Tsare-Tsaren Tattalin Arziƙi, Atiku Bagudu wanda ya yiwa manema labaran fadar gwamnati jawabi ta na’ura yace daga cikin gwamnonin Najeriya 36, har yanzu gwamnonin jihohi 20 da birnin tarayya, Abuja, ba su bayyana matsayarsu ba.

Saidai bai fayyace sunayen jihohin ba

Gwamnonin da suka gabatar da matsayarsu a rubuce sun kuma buƙaci a yiwa kundin tsarin mulkin ƙasar garanbawul.

A wani labarin kuma, Majalisar Tattalin Arziƙin ta kuma karɓi taƙaitaccen rahoton wucin gadi akan matsalar satar ɗanyen mai da hanyoyin maganceta

Kwamitin ya fayyace wuraren da ake samun zurarewa a ɓangaren albarkatun man fetur a yayin da ya tantance wuraren da ake yawan samun karya doka.

Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya buƙaci samun ƙudirin gwamnati wajen aiwatar da sauye-sauye.

Leave a Reply