Rashin tsaro: Gwamnatin Najeriya ta rufe makarantun sakandire mallakin Gwamnatin tarayya
Gwamnatin Taraiya ta bayar da umarnin rufe illahirin makarantun sakandare mallakin ta, waɗanda ake kira da Unity Schools har guda 41 da ke ƙasar.
BBC ta rawaito cewa hakan ya biyo bayan damuwar da ake da ita game da yadda matsalar sace ɗaliban makarantu ta sake kunno kai a Najeriya.
Ma’aikatar ilimi ƙasar ce ta fitar da sanarwar rufe makarantun.
Sanarwar ta ce ministan ilimi na Najeriya, Tunji Alausa, ne ya bayar da izinin rufe makarantun haɗakar arba’in da daya na tarayya, ba tare da ɓata-lokaci ba.
KU KUMA KARANTA: Gwamnatin tarayya ta fitar da Naira Biliyan 2.3 don biyan bashin Malaman Jami’a
Ministan ya ce sakamakon sabon ƙalubalen tsaro da ya kunno a wasu sassan Najeriya dole a ɗauki matakin da ya dace kuma a matsayin wani kandagarki.
Sanarwar ta kuma buƙaci shugabannin makarantun da abin ya shafa da su tabbatar da aiwatar wa tareda bin wannan umarni sau da ƙafa.
Ko da yake sanarwar ta yi nuni da cewa rufe makarantun na wucin gadi ne, sai dai ba ta sanar da ranar da za a buɗe su ba.









