Rasha ta yi atisayen harba makamin nukiliya

0
168

Ƙasar Rasha ta gudanar da atisayen soji domin tabbatar da cewa tana cikin shirin iya kai gagarumin farmakin nukiliya a cewar ministan tsaron ƙasar, Sergei Shoigu.

Atisayen ya haɗa da “martani kan harin makamin nukiliya daga maƙiya”, in ji ministan tsaron.

Kafar talabijin ta ƙasar ta nuno ministan yana yi wa shugaba Putin bayani kan atisayen.

Lamarin ya zo ne daidai lokacin da majalisar dokokin ƙasar Rasha ta goyi bayan janyewar da ƙasar ta yi daga yarjejeniyar ƙasa da ƙasa kan haramta gwajin makaman nukiliya.

KU KUMA KARANTA: Rasha ta harbo jiragen Yukiren marasa matuƙa 31 a yankunan kan iyaka

Rasha da Amurka sukan yi atisayin gwajin makamin nukiliya a kai-a kai, inda Rasha ta saba yin nata a ƙarshen watan Oktoba.

Sanarwar da Kremlin ta fitar ta ce atisayen na baya-bayan nan sun haɗa da harba nau’uka daban-daban na muggan makamai masu linzami, waɗanda suka haɗa da makami mai linzami da ake iya amfani da shi wajen kai hari tsakanin nahiyoyi da makami mai linzami da aka harba daga wani jirgin ruwa mai ƙarfin nukiliya.

Leave a Reply