Ranar Juma’ar wannan mako za a shafa fatihar auren mutum 1,800 da gwamantin jihar Kano ta ɗauki nauyi.
Gwamnatin Kano ta sanar cewa a ranar Juma’ar makon nan, 13 ga Oktoba za a ɗaura auren zawara a ƙarƙashin shirinta na auren gata.
Gwamna Abba Kabir ne ya sanar da ranar ɗaurin auren bayan ran gadinsa tsare-tsaren da Hukumar Hisbah ta jihar ta yi domin ɗaurin auren a ofishinta.
Mutum 1,800 ne za su ci gajiyar auren gatan, wanda suka haɗa da zawarawa da naƙasassu da masu ƙaramin ƙarfi, daga ƙananan hukumomi 44 ta jihar, kamar yadda gwamnatin ta sanar.
Gwamnan ya yaba da yadda Hisbah ta yi tsarin, musamman ganin yadda auren gatan ya ƙunshi masu ƙaramin ƙarfi da kuma naƙasassu.
KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe ya rattaɓa hannu kan zartar da hukumar Hisbah da YITDA a jihar
Ya kuma yi alƙawarin ba wa hukumar duk kulawar da ta dace, inda ya nuna ɓacin ransa da rashin kammala gine-ginen da ke ofishin hukumar a tsawon shekaru takwas na gwamnatin da ta gabata.
Da yake jawabi, babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce lokacin da aka ɗauki nauyin auren gatan da za a yi ya yi daidai, saboda ya kawo wa masu son aure sauƙi, sannan zai rage matsalar zinace-zinace.