Ranar Alhamis za a ci gaba da shari’ar Shaikh Abduljabbar kan hukuncin kisa

0
103

Daga Ibraheem El-Tafseer

Kotun ɗaukaka ƙara dake zaman ta a sakatariyar Audu Baƙo a Kano, ta ɗage ci gaba da sauraren shari’ar da Abduljabbar Nasir Kabara, ya ɗaukaka kan hukuncin kisa ta hanyar rataya, da babbar kotun shari’ar addinin musulunci dake zaman ta a Ƙofar Kudu, ta yanke masa bisa zarginsa da laifin yin ɓatanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.

Kotun ɗaukaka ƙarar ƙarƙashin jagorancin, Justice Nasiru Yusuf da kuma A’isha Mahmud , sun saurari ƙarar a ranar Litinin ɗin nan.

Lauyan Abduljabbar Nasiru Kabar, Barista Yusuf Sadik, ya shaida wa kotun cewar a shirye suke don ci gaba da sauraren shari’ar.

KU KUMA KARANTA: Yadda ta kasance a babbar kotun Kano kan sauraren ƙarar da Mal. Abduljabbar ya shigar

Sai dai lauyan gwamnatin Kano Barista Bashir Saleh, ya roƙi kotun da ta ƙara musu lokaci kafin a ci gaba da sauraren shari’ar.

Lauyan Abduljabbar Nasiru Kabara, ya nuna rashin jin daɗinsa, sakamakon yace tun tuni ya sada lauyan gwamnatin da takaddun martaninsu tun a watan Fabarairun 2024, inda ya nemi gwamnatin Kano ta biyashi naira miliyan 20, sakamakon ɓata masa lokaci da aka yi.

Alƙalan kotun, Justice Nasiru Saminu da Justice A’isha Mahmud, sun bincika takardun da lauyan Abduljabbar Nasiru Kabara, ya yi iƙirarin ya sadar da lauyan gwamnatin Kano, inda aka gano cewar a watan Maris ya ba wa lauyan gwamnatin takardun martanin .

Daga bisani lauyan Abduljabbar Nasiru Kabara, ya janye buƙatar Neman Gwamnatin ta biya shi naira miliyan 20.

Alƙalan kotun ɗaukaka ƙarar sun ɗage ci gaba da sauraren shari’ar, zuwa ranar 9 ga watan Mayun 2024, don ci gaba da sauraren shari’ar.

Leave a Reply